5 Afirilu 2020 - 07:25
 Turkiya Ta Aike Da Karin Sojoji Zuwa Yankin Idlib Na Kasar Syria

Turkiyan ta tura Karin sojojinta ne dai zuwa yankin na Idlib da ke arewa maso yammacin kasar Syria a ci gaba da kokarin da Ankara take yi na tabbatar da ikonta a yankin.

(ABNA24.com) Turkiyan ta tura Karin sojojinta ne dai zuwa yankin na Idlib da ke arewa maso yammacin kasar Syria a ci gaba da kokarin da Ankara take yi na tabbatar da ikonta a yankin.

Hukumar kare hakkin dan’adam ta kasar Syria ( SOHR) ce ta bayyana haka, tana mai kara da cewa; Sojojin da Turkiyan ta tura sun hada da motocin yaki 35 da suka ketara iyaka suka bi ta hanyar Kafar Lusin a jiya juma’a.

A ranar Alhamis din da ta gabata ma dai sojojin na Turkiya sun kai farmaki akan sansanin sojan Syria a kauyen Hassan da ke yammacin garin Manbij.


/129